China ta zarta bankin duniya wurin bada rance

Image caption Kudin kasar china

Rahotanni sun ce China ta zarta bankin duniya wurin ba da rance ga kasashe masu tasowa.

Binciken jaridar Financial Times, ya ce bankin cigaban kasashe na China da kuma bankin kasuwanci na kasa da kasa, sun ba da bashin akalla dala biliyan dari da goma cikin shekaru biyun da suka wuce

Ana dai ganin hakan ya zarta basussukan da bankin duniya ya bayar, da kimanin kaso goma cikin dari.

Wakilin BBC ya ce bankunan na China na bada basussuka ne ga kasashen da ke samar da kayayyakin sarrafawa a masana'antu, a lokacin da samun rance ke matukar wahala.

Hakan na baiwa kasar damar kulla yarjejeniya mai dogon zango, kan samun makamashi ciki har da man fetur daga Rasha, Venezuela, da kuma Brazil.