Takaitaccen tarihin Malam Nuhu Ribadu

Nuhu Ribadu
Image caption Nuhu Ribadu ya yi alkawarin kafa sabuwar Najeriya

An haifi Malam Nuhu Ribadu a ranar 21 ga watan Nuwamban 1960.

Ya samu shaidar digiri ta farko a fannin ilimin shari'a daga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1983.

Ya kuma karbi shaidarsa ta zama lauya a shekara ta 1984.

Malam Nuhu Ribadu ya kara halartar jami'ar Ahmadu Bello domin karatun digiri na biyu a fannin na shari'a.

Sannan ya halarci sashin kasuwanci na jami'ar Harvard da ke Amurka.

Daga nan ne kuma ya fara aiki da Hukumar 'yan sandan Najeriya, inda ya ci gaba da aiki a matakai daban-daban, har ya zamo shugaban bangaren shari'a da gabatar da masu laifi a ofishin Hukumar da ke Abuja.

Shekaru 18 din da ya shafe yana aiki a Hukumar 'yan sandan Najeriya, ya kai har aka nada shi shugaban Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) a watan Afrilun shekara ta 2003.

Yana cikin kwamitin tattalin arziki da shugaba Obasanjo ya kafa a shekara ta 2003 zuwa 2008, wanda ya haifar da sauye-sauyen da aka gudanar a bangarori daban daban na kasar.

Nasarar da ya samu ta hadar da cire Najeriya daga jerin kasashen da ba sa bada hadin kai ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa.

A watan Oktoban 2007 ne kuma tsohuwar gwamnatin shugaba Umaru 'Yaradua ta cire shi daga shugabancin Hukumar ta EFCC, sannan aka tura shi ya karo karatu.

Amma daga bisani abin ya bige cikin rudani, inda ya yi sanadiyyar korarsa daga aiki.

Matakin da daga bisani aka mayar zuwa ritaya.

Wannan lamari ya tilasta wa Ribadu yin gudun hijira na kashin kansa zuwa Amurka da Burtaniya, inda ya yi karatu a jami'ar Oxford ta Burtaniya, da kuma Center for Global Development a Amurka.

Bayan dawowar sa Najeriya daga Amurka, sai gwamnatin shugaba Goodluck ta sauya korar da aka yi masa zuwa ritaya tare da mayar masa da mukaminsa na mataimakin shugaban 'yan sanda.

Malam Nuhu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a watan Afrilu karkashin jam'iyyar adawa ta ACN a a watan Disambar 2010.

Kuma a watan Janairun shekara ta 2011 ne, jam'iyyar ACN ta tsayar da shi a matsayin dan takararta a zaben na watan Afrilu mai zuwa.

Zai dai fafata ne tare da shahararrun 'yan takara da suka hada da shugaba Goodluck na jam'iyyar PDP da Janar Buhari na CPC da kuma Gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau na ANPP.

Karin bayani