An umurci soji da su bindige masu tayar da zaune tsaye a Jos

Rundunar tsaro ta musamman a jahar Pilato, ta ba jami'anta umurnin su bindige duk wani mutum da ke kokarin tada zaune tsaye.

Rundunar ta ce daukar matakin ya zama wajibi, saboda matasa a birnin Jos basa jin rarrashi, yayin da suke kona wuraren ibada da dukiyar jama'a ba gaira babu dalili.

Umarnin dai ya biyo bayan taho mu gamar da aka yi jiya a Jos, tsakanin wasu matasa da sojoji, inda aka sami hasarar rayuka da kuma jikkata.