Wani ya banka wa kansa wuta a Masar

Jami'an kasar Masar sun ce wani mutum wanda ya bankawa kansa wuta akan rufin gidansa a birnin Iskandiriya, ya mutu a sanadiyar raunikan da ya samu.

Jami'ai sun ce mutumin, dan shekaru 25 da haihuwa ya shafe shekara guda ba shi da aikin yi, sannan kuma yana fama da tsananin damuwa.

Matakin da ya dauka ya yi kama da abun da ya faru a Tunisia, wanda kuma ya kai ga yi wa gwamnatin bore, har ya tilasta wa shugaban kasar sauka daga kan karagar mulki.

Wannan dai shi ne mataki irinsa na baya bayan da ya afku a kasashe kamar Masar da Algeria da Mauritania.

Jami'ai sun kara da cewa akwai wani mutum wanda shi ne na biyu a cikin kwanaki biyu da ya bankawa kansa wuta a kofar ginin majalisar dokoki a birnin Alkhahira.