Gwamnatin Nijar ta musanta yi wa 'yan takara sassauci

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta musanta cewa, shugaban kasar Janar Salou Djibo, ya kara wa'adin yin rajistar masu neman tsayawa takarar majalisar dokokin kasar.

A jiya ne aka bada sanarwar kara wa'adin da kwana ukku, bayan muhawarar da aka gudanar a makon jiya, a karkashin inuwar kungiyar sasanta rikicin siyasa ta CNDP.

Kotun tsarin mulkin kasar ce ta yi watsi da takardun 'yan takarar, saboda ba su cika wasu ka'idoji ba, wanda hakan ya sa wasu jam'iyyu ba za su yi takara a wasu jihohi ba.

A karkashin tsarin dokokin jamhuriya ta bakwai dai, babu wani wurin daukaka kara idan kotun tsarin mulkin ta yanke hukuncinta.