Maganar kawance tsakanin CPC da ACN na nan daram

Image caption Tutar jami'yyar adawa ta ACN

Jam'iyyar Adawa ta CPC a Nigeria ta ce maganar kawancen ta da jam'iyyar ACN na nan daram.

Sakataren jam'iyyar na kasar Injiniya Buba Galadima ya ce duk da cewa jam'iyyun biyu, sun gudanar da zabukan fidda 'yan takarar su na shugaban kasa amma hakan ba zai kawo wata tagarda ba a tattaunawarsu

Ya kuma ce maganar kawance tsakanin jamiyyun biyu maganace kawai ta lokaci.

Wannan tabbaci da jam'iyyar ke bayarwa dai na zuwa ne dai-dai lokacinda zaben kasar ke kara karatowa.