Shugaban PDP na kasa ya yi murabus

Tsohon shugaban PDP Dr Ezekwesili Nwodo
Image caption Tsohon shugaban ya dade yana fuskantar matsin lamba kan ya yi murabus

Shugaban jam`iyyar PDP mai mulkin Najeriya Dr Ezekwesili Nwodo ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon matsin lambar da yake fuskanta.

Tuni dai Kuma Majalisar zartarwar jam`iyyar wadda ta kammala zaman ta na gaggawa a Abuja ta amince da murabus din shugaban.

Farfesa Rufa`i Ahmed Alkali shi ne Kakakin jam`iyyar na kasaya shaida wa wakilin BBC Ibrahim Isa cewa, halayyar da shugaban ya nuna a wurin taron fitar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ne ya sa shi yin murabus.

A yanzu kwamitin zartarwa na jam'iyyar ya umarci mataimakin shugaban na kasa Dr Bello Halliru da ya ci gaba da rike mukamin na wucin gadi.

Haka kuma an nemi tsohon shugaban ya gurfana a gaban kwamitin da'a na jam'iyyar domin bada ba'asi kafin a duba hukuncin da ya kamata a dauka a kansa.