Har yanzu tsugune ba ta kare wa shugaban PDP ba

Shugaban PDP Okwesilieze Nwodo
Image caption Shugaban PDP Okwesilieze Nwodo ya dade yana fuskantar matsaloli

A Najeriya, wata sabuwar badakala ta kunno kai dangane da batun ci gaba da zaman Dokta Okwesilieze Nwodo a matsayin shugaban jam'iyyar PDP na kasa.

Inda wasu kusoshin jam'iyyar a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar, suka nemi a yi biris da bukatar tsige shugaban jam'iyyar na kasa daga mukaminsa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin zartas wa na jam'iyyar ke taron gaggawa a Abuja, domin duba halin da jam'iyyar ke ciki.

Ana saran kwamitin zai maida hankali kan rikice-rikicen da suka dabai baye jam'iyyar sakamakon zabukan fatar da 'yan takarkaru a sassa daban daban.

Wannan sanarwa ta zo ne kwana daya, bayan da wasu shugabannin jam'iyyar ta PDP a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya, suka bayyana rashin gamsuwarsu da shugaban jam'iyyar na kasa.

Sakamakon zargin da suke yi masa, na yin watsi da kundin tsarin mulkin jam'iyyar, da rashin yin biyayya ga umarnin kotu, ta hanyar bayyana a wajen babban taron jam'iyyar na kasa, wanda aka gudanar a makon da ya gabata a Abuja.

Masu lura da al'amura dai, na ganin wannan sabuwar badakala, ba ta rasa nasaba da tsamar da ake zargin ta shiga tsakanin bangaren shugaban jam'iyyar PDPin na kasa, da kuma wasu kusoshin jam'iyyar a Kudu maso Gabashin Najeriya, a cewar wakilin BBC a Enugu AbduSsalam Ahmed Ibrahim.