Yan adawa sun shiga gwamnatin rikon kwaryar Tunisia

Rikicin siyasa a Tunisia
Image caption Tarzomar siyasa ce ta haifar da rushewar tsohuwar gwamnatin Ben Ali

An kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Tunisia bayan hambarar da shugaba Zainul Abidina Bin Ali, inda aka baiwa jagororin 'yan adawa kujeru uku a majalisar ministoci.

Dan adawar nan mai baiyana ra'ayinsa a shafin intanet, Salim Amamou, wanda aka tsareshi lokacin rikicin baya-bayan nan, na cikin ministocin da aka nada, inda aka bashi ma'aikatar matasa da harkokin wasanni.

Sai dai har yanzu magoya bayan Mr Ben Ali ne ke rike da ma'aikatun tsaro, da harkokin cikin gida, da kudi, da kuma hulda da kasashen waje.

Wasu daga cikin 'yan adawar kasar sun ce wadannan sauye-sauyen ba su wadatar ba, inda suka bukaci a tarwatsa tsohuwar jam'iyyar da ke mulkin kasar baki daya.

Hakazalika jama'ar kasar sun ce sabon kundin tsarin mulkin kasa suke so