'Yan adawa sun fice daga sabuwar gwamnatin Tunisia

Image caption Pira Minista Mohammed Ghannouchi

Rohatanni daga Tunisia na nuni da cewa Ministoci uku sun fice daga sabuwar gwamnatin hadin gwiwar kasar.

Ministocin dai na jam'iyyar adawa ce ta General Union of Tunisian Workers wato UGTT wacce ta taka mahimmiyar rawa a zanga-zangar da ta sanya tsohon shugaban kasar, Ben Ali ya sauka daga kujerarshi.

Masu zanga-zangar dai sun fusata ne bayan da Pira Minista Mohammed Ghannouchi ya mayar da wasu Ministocin da su ka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaba Ben Ali.

Gwamnati ta amince cewar wajen mutane 78 ne su ka mutu a zanga-zangar da aka yi ta tsawon wata guda.

Mr Ghannouchi ya bayyana sabuwar gwamnatin ranar Talata wacce ta hada da 'yan adawa a cikinta da kuma tsaffin jami'an tsohuwar gwamnatin.

Amma wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ki amince wa da sabuwar gwamnatin, inda su ke neman a cire wasu daga cikin jami'an tsohuwar gwamnatin da ta shude.

Karin bayani