Raila Odinga ya ziyarci Ghana

Fira Ministan kasar Kenya Raila Odinga
Image caption Wannan ne karo na biyu da Raila Odinga ke ziyartar kasar Ivory Coast

Fira Ministan kasar Kenya Raila Odinga wanda ke shiga tsakani a rikicin siyasar kasar Ivory Coast ya isa kasar Ghana domin tattaunawa da shugaba John Attah-Mills.

Mr Odinga ya nuna rashin jin dadinsa game da rashin samun cikakkakiyar nasara a shiga tsakanin da yake yi, inda ya kara da cewa lokaci na kurewa Luarent Gbagbo.

Raila Odinga ya ziyarci kasar ta Ivory Coast a karo na biyu bayan da Tarayyar Afrika ta tura shi domin ya sasanta rikicin siyasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Mista Odinga ya shaida wa manema labarai a kasar cewa babu ci gaba da aka samu a yunkurin sasanta rikicin kasar ta Ivory Coast.

Yace ya bai wa Laurent Gbagbo damarmaki har uku, wadanda suka hada da janye kawanyar da aka yi wa otel din da Alassan Outarra ke zaune.

Kuma yana da damar zuwa gudun hijira a kasashen nahiyar, ba tare da an tuhume shi ba.

Har ila yau Ghana ta ce tana goyon bayan shirin kungiyar Ecowas na amfani da karfi wajen kawar da Laurent Gbagbo, amma ba ta da isassun sojojin da za ta bayar gudummawa.

Shi dai Laurent Gbagbo ya ki sauka daga mulki, duk da cewa abokin hamayyar sa Alassan Outarra ne kasashen duniya su ka amince ya lashe zaben.