An gurfanar da tsohon shugaban kasar Haiti gaban kuliya

Haiti
Image caption Kwananan ne tsohon shugaban Ya koma kasar ta Haiti daga gudun hijira

Masu shigar da kara a Haiti na tuhumar tsohon shugaban kasar Jean-Claude Duvalier da laifin sata da barnatar da dukiyar al'umma a zamanin mulkinsa na shekaru goma sha biyar da ya kare a cikin alif dari tara da tamanin da shida.

An dai gurfanar da Mr Duvalier ne da aka fi sani da Baby Doc, kwanaki biyu da komawar bazatar da ya yi Haiti bayan gudun hijirar shekaru ashirin da biyar.

Yanzu dai ana jiran alkali ya duba yiwuwar gudanar da cikakkiyar shari'a kan batun.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama dai na son a kara laifuffukan azabtarwa da kisan dubunnan mutane, cikin jerin abubuwan da ake tuhumar Mr Duvalier.

Sai dai Maitre Gervais Charles, wani babban lauya a Haiti kuma daya daga cikin masu kare Mr Duvalier, ya shaidawa BBC cewa ya na da tabbacin tsohon shugaban kasar ba zai kai ga shiga kurkuku ba.