Man City ta doke Leicester a gasar FA

Man City ta doke Leicester a gasar FA
Image caption A yanzu Manchester City za ta kara ne da Notts County a zagaye na gaba

Sven-Goran Eriksson bai koma Eastlands da kafar dama ba, bayan da Manchester City ta lallasa kungiyarshi ta Leicester da ci 4-2 a zagaye na uku na gasar FA.

Carlos Tevez ne ya zira kwallon farko a wasan kafin Paul Gallagher ya rama wa Leicester.

Kwallaye biyun da Patrick Vieira da Adam Johnson su ka zira a minti daya da rabi - sun bai wa City tazara a wasan, kafin Tavez ya barar da fanareti.

Kwallon da Lloyd Dyer ya zira ta bai wa Leicester kwarin gwiwa, sai dai Aleksandar Kolarov bai bari ta kawana ba, inda ya zira wa City kwallo ta hudu.

A yanzu Manchester City za ta kara ne da Notts County na League One, a zagaye na hudu na gasar ta FA.