Zabukan jamhuriyar Nijar

Image caption Masu kada kuri'a

Wani fitaccen dan takara a zaben shugaban kasar da za'a yi karshen watan nan a jamhuriyar Nijar, Malam Sani Mahamane na jam'iyyar MDN ya ce shi da wasu 'yan takarar, sun bukaci a dage zaben da makonni uku bayanda aka fuskanci matsala da zaben kananan hukumomi a farkon watan nan.

Malam Sani Mahamane ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa jam'iyyun na neman a dage zaben ne zuwa ashirin ga watan Fabrairun gobe, saboda rashin amincewa da hukumar zabe ta kasar.

Za'a dai gudanar da zaben ne domin mai da Nijar mulkin farar hula bayanda sojoji su ka hambarar da gwamnatin Malam Tandja Mammadou kusan shekara guda kenan bisa laifin Ta-zarce

Hakazalika a jiya ne mai shiga tsakani a rikicin siyasar kasar, tsohon shugaban Najeriya janar Abdusalami Abubakar ya tattauna da 'yan takarar shugabancin kasar su goma da zummar samar da hanyoyin shirya zabubbuka masu zuwa cikin tsanaki.