Rigingimu a jam'iyyar CPC

Image caption Janarar Muhammadu Buhari

Rigingimun cikin gida na kara ruruwa a jam'iyyar adawa ta CPC a Najeriya,inda a wasu jihohi 'yan jamiyyar ke cigaba da kokawa bisa abinda suka ce rashin adalci wajen gudanar da zabubbukan fid da gwani na jam'iyyar.

A jihar Kaduna rashin jin dadin yadda aka gudanar da zabubbukan fid da gwanin, musamman na mukamin gwamna ya haifar da korafe korafen da suka janyo ficewar daya daga cikin manyan 'yan jamiyyar tare da magoya bayansa daga CPC.

Honrable Sani Sha'aban wanda ya tsaya takarar mukamin gwamnan jihar Kaduna karkashin innuwar jamiyyar CPC ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben fidda da gwani na jami'yyar

Sai dai uwar jamiyyar ta musanta haka, ta kuma ce nan bada jimawa ba, zata sanar da wadanda suka samu nasara a zaben fid da gwani, a wasu jihohin da aka samu takkadama.

Jihohin dai sun hada da Katsina, da kano,da Sokoto da kuma Bauchi.