Mun gano bakin zaren inji hukumar zaben Najeriya

Image caption Farfesa Attahiru Jega

Hukumar zaben Nigeria, INEC ta ce 'yan Nigeria su sha kuruminsu dangane da cikas din da ake samu wajen yiwa masu kada kuri'a rajista a kasar.

Shugaban hukumar farfesa Attahiru Jega ya ce abubuwa sun fara inganta yayinda su ka fara shawo kan matsalar.

Ya ce sun baza ma'aikanta cikin kasar domin a gyara naurorin.

A ranar asabar din ta gabata ne aka fara sabunta rajistar masu zabe a fadin kasar a shirye-shiyen da ake yi na zaben gama gari da za'a gudanar a watan Aprilu mai zuwa.

Sai dai aikin ya gamu da tsaiko, inda a sassan kasar da dama ake samun rahotannin matsaloli dabam dabam da suka hada da tafiyar hawainiya da aikin ke fuskanta musamman ma tangardar na'ura.