Yan adawa sun nuna shakku

Image caption Aikin sabunta rajistar masu zabe

Sakamakon matsalolin da suka dabaibaye aikin rajistar masu jefa kuri'a da ake yi a Nijeriya, yanzu haka wasu 'yan-adawa a kasar sun fara nuna shakku kan yiwuwar gudanar da zabuka na gaskiya a watan Afirilu mai zuwa.

'Yan adawar dai na cewa ba a bin tsarin da aka tanada na yin rajistar, kuma suna ganin wannan wani mataki ne na tafka magudi a zabukan.

Sai dai hukumar zabe ta kasar ta ce an shawo kan mataslolin kuma ba zasu shafi ingancin zabukan ba.

A hirar da yayi da BBC shugaban hukumar Zaben Farfesa Attahiru Jega ya bada tabacin zasu yi biyaya kan dokokin zaben kasar kuma za'a hukunta duk wani wanda aka kama da laifin aikata magudi.

A ranar Asabar ne aka fara rajistar masu jefa kuri'a inda aka sami matsalolin da suka hada da rashin ingancin kayan aiki, da karancin kayan aikin da kuma rashin samun ma'aikata a wasu wurare.