Murabus din Dokta Nwodo na ci gaba da janyo cece - ku- ce

Saukar Dokta Okwesilieze Nwodo daga mukamin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ta jawo cece-ku-ce a shiyyar kudu maso gabashin kasar, wato yankin da tsohon shugaban jam'iyyar ya fito.

Yayin da wasu ke ganin saukar Dokta Nwodo daga mukamin na sa ta dace, kuma wani ci gaba ne ga jam'iyyar, wasu kuwa illar hakan suke gani.

A jiya ne dai Dokta Nwodo ya yi mirabus daga mukaminsa a lokacin da aka kira taron kwamitin zartaswa na jama'iyar don tattaunawa kan matsayinsa a jama'iyar bayan da wata kotu ta dakatar da shi a jajibirin babban taronta