Majalisar dinkin duniya za ta tura ayarinta zuwa Tunisiya

Majalissar dinkin duniya ta ce za ta tura wani ayarin ma'aikatan kare hakkin jama'a zuwa Tunisia, domin baiwa sabuwar gwamnatin kasar Shawara, tare kuma da gudanar da bincike akan mummunan tashin hankalin da ya afku a kasar.

Babbar Kwamishiniyar MDD mai kula da kare hakkin jama'a Navi Pillay, ta ce ofishinta ya samu bayanai masu tada hankali.

Ta ce, "ofishina ya samu bayana akan cewar mutane fiye da dari sun mutu a cikin makonni biyar da suka wuce, a sakamakon harbi, da kuma masu kashe kansu da kansu domin nuna rashin amincewarsu da abun da ke faruwa da kuma mummunar tarzomar da aka yi a karshen mako."

Ms Pillay ta bayyana cewar keta hakkokin bil-adama sune makasudin irin matsalolin da ake fuskanta a Tunisia, to amma ta kara da cewar a nan gaba, kamata yayi a hukunta duk wani wanda aka samu da laifi daga shugaban kasa zuwa ga ma'aikatan tsaro da ke kan tituna.