Dangantaka tsakanin China da Amurka

Image caption Shugaba Hu Jintao

Shugaban kasar China Hu Jintao da takwaransa na Amurka Barak Obama sun ci abincin dare tare a fadar White House a farkon wata ziyarar yini hudu zuwa Amurka.

Ganawar ta su na zuwa ne kafin liyafar cin abincin dare ta alfarma da aka shirya yi a yau Laraba.

Ziyarar ta Mr Hu da aka ce ita ce mafi muhimmanci cikin shekaru talatin, na zuwa ne daidai lokacinda ake samun karin sabani tsakanin kasashen biyu game da ciniki da kuma darajar kudi, inda Amurka ke bukatar China ta kyale darajar kudinta na Yuan ta hauhawa.

An dai sha kiran kasahen biyu abokanan hammayar juna amma a jawaban da aka gabatar gabanin ziyarar, jami'an gwamnati sun jaddada irin ribar da Amurka zata samu a huldar dake tsakanin ta da China.

Kashi hudu na yawan basussukan Amurka na hannun China amma gwamnatin Amurka ta ce komai na tafiya dai dai wajen fitar da kudi fiye da dala biliyan dari zuwa Chinar a shekarar da muke ciki.