Tony Blair ya sake baiyana gaban kwamitin bincike

Tsohon firaministan Burtaniya Tony Blair ya sake baiyana gaban hukumar binciken rawar da kasar ta taka a yakin Iraqi.

An yi sammacin Mr Blair ne domin yin bayani game da gibin da aka samu a shaidar da ya bayar a baya, da kuma bambance-bambancen da ke tsakanin bayaninsa da takardun gwamnati da ma bayanan wasu shaidu.

Hukumar binciken ta yi mishi tambaya ne game da alkawurran da ya yi wa tsohon shugaban Amurka George W Bush da kuma yadda ya yi amfani da shawarwarin da ya samu game da halaccin yakin.

A gurfanar da ya yi gaban hukumar a bara dai, Mr Blair ya kare matakin da ya dauka na marawa Amurka baya a yakin inda ya ce ya yi ammana duniya zati fi samun lafiya idan ba Saddam Hussein.

Za'a mu kawo muku karin bayani