Sabon kundi ga yan takarar Nijar

Image caption Jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar kungiyar nan ta Amurka mai fafutukar yada demokaradiya a duniya NDI tare da hadin gwiwar majalisar sasanta rikice rikicen siyasa CNDP sun fito da wani kundi da suka kira na da'a da bin doka .

Kundin ya kunshi matakai daban daban da ya dace 'yan siyasa masu takara su kiyaye da su don kaucewa rigingimu a lokacin zabubbuka.

Yan takarar dai zasu alkawarin da zai sa su rika kira ga magoya bayansu su kaucewa tashe tashen hankula.

Malam Abba Gana daga jami'yyar R-S-D gaskiya wanda ya halarci taron ya shaidawa BBC cewa sun gamsu da kudurin kuma zai kawo zaman lafiya a lokacin zaben.

Sai dai Malam Tambura Issoufou sakataren yada labarai na jami'yyar M-S-N-D nasara cewa ya yi an kawo likita ne bayan mutuwa, saboda sun wuce abin da ke cikin kundin akan haka daukar alkawari ba zai wani tasiri ba wurin hana magudi a lokacin zabe.