Kotun koli a Nijar ta garkame sojojin nan 4 da ake zargi da juyin mulki

Kotun kolin Jamhuriyar Nijar ta yanke hukuncin ci gaba da tsare hafsoshin sojojin nan hudu da gwamnati ke zargi da yunkurin juyin mulki a gidan kukrkuku.

Daukar wannan mataki da kotun ta yi dai ya biyo bayan soma sauraren karar da hukumomin majalisar mulkin sojan kasar ta CSRD suka shigar a kan su .

Lauyoyin sojojin dai sun ce za su ci gaba da gwagwarmayar domin kwato masu yancinsu.

Gwamnati na zargin wadannan hafsoshin sojoji da suka hada da tsohon na hannun damar shugaban kasar, kanar Abdullahi Bague da tsohon Ministan ayyuka, kanal Diallo Amadou da laifin yi wa kasa zagon kasa.

An dai cabke wadannan sojoji ne tare da tsare su tun a watan Oktoban da ya gabata.