Hadin kan 'yan siyasa da al'ummar Niger

Yayinda ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zabubbuka na kasa a jamhuriyar Nijar, maganar rarabuwar kawunan 'yan siyasa, ko kin cika alkawuran da sukan yi wa al'umma, na ci gaba da jefa kasar da ma al'ummar ta cikin halin rashin kwanciyar hankali.

Hakan ne ma ke sanya wa wasu suna gudanar da zanga-zanga, yake-yaken tawaye ko kuma juyin mulki.

Wasu karin kalubale da hukumomi a kasar ke fuskanta sun hadar da sace-sacen mutane ko ayyukan ta'addanci da kungiyar Alqaeda ke gudanarwa a wasu yankunan kasar.

Tun da kasar ta koma ga bin tafarkin demokradiya shekaru 20 da suka gabata, ta sha kwan gaba kwan baya ta fannin rigingimun siyasa ko rashin kwanciyar hankali a wasu sasan kasar, kamar jihar Agadez wacce a baya ta so ta balle domin kafa tsarin mulki irin na Fediraliyya.

Rashin hadin kan 'yan siyasa

Galibin 'yan Niger din na danganta ire-iren wadannan matsaloli da rashin hadin kai ko rashin kishin kasa ga wasu 'yan siyasa.

Malam Siraj Isaka, wani dan gwgwarmayar kungiyoyin farar hula ne a Niger, ya ce; "Talakawan Niger a karkara basu da matsala, basu da wariya basu da bambanci. Amma matsalar siyasa a Niger 'yan takarda ne da yan siyasa. Kuma har abada ba za'a samu kwanciyar hankali a Niger ba tunda kowanne dan siyasa kansa yake so. Kuma kaga idan akwai zancen son kai kenan zancen son kasa bai taso ba."

Sai dai wasu 'yan Niger sun nuna bambancin ra'ayi kamar yadda wani mutum ya shaida wa wakilin BBC; "A yanzu kam zan iya cewa akwai hadin kan 'yan kasa. Babu wani bambanci, Mutane duk daya suke. Addini, da aure da karatu sun kara hada kan 'yan kasa kuma suna sa, a san juna, a kusanci juna kuma a raga wa juna."

Sai dai 'yan siyasa kamar su Hajiya Hafsatu Magaji daga jamiyyar MNSD Nasara na masu kare matsayar su da cewa; "To wane ne kuwa ke iya hada kan 'yan kasa face 'yan siyasa?."

"Lura da kyau, bayan hambarar da mulkin mu, kaji MNSD Nasara ta yi wani motsi? Ba mu kawo wata fitina ba."

"Ai badan abin bai yi mana ciwo ba, amma babbar jam'iyya kamar MNSD, bai dace ta kawo wata matsala ba muddin dai demokradiya ake yi, wannan kuwa mun yi ne, saboda kishin kasa da muka gada a cikin kundin tsarin jam'iyyar mu." Shi kuwa Mallam Abubakar Suley Na Nalado, shugaban jamiyyar Borkulu-Wane,NA KOWA ce wa ya yi; "Kamata ya yi tunda wannan iko ya hau ya kira kowa da kowa domin zantawa ba tare da ya nuna wancan dan AFDR ne ko wannan dan CFDR ne, ko wadancan 'yan bangaren 'yan ba ruwanmu ne, a hadu kowace jam'iyyar siyasa ta tofa albarkacin bakinta a cikin tafiyar da muhawarar ginin kasa."

Sai dai ko bayan wadannan rigingimmu na siyasa da kasar Niger din ta sha fuskanta wadanda ma suka dinga baiwa sojoji damar dira a cikin fagen siyasa ta hanyar juyin mulki kamar a 1996 da 1999 da kuma 2010, wasu karin matsalolin da Niger din ke cin karo da su su ne na sace-sacen mutane tare da hallaka wasu, da kungiyar AQMI reshen ALQAEDA ke aikatawa .

Hakan dai ba shakka, zai kasance wani babban kalubale ga sabbin shugabbanin da za'a zaba nan gaba.