An fara shariar hafsoshin sojan nan dake tsare a Nijar

Wasu sojojin Nijar
Image caption Wasu sojojin Nijar

A jamhuriyar Niger a yau ne babbar kotun kasar ta fara sauraren karar da majalisar mulkin soja ta CSRD ta shigar a kan wasu hafsoshin sojojin kasar su hudu.

Gwamnati na zargin wadannan hafsoshin sojoji da suka hada da tsohon na hannun damar shugaban kasar, kanar Abdullahi Bague da tsohon Ministan ayyuka, kanal Diallo Amadou da laifin yi wa kasa zagon kasa.

Sai dai lauyoyin da ke ba su kariya a gaban kotu sun yi watsi da wannan zargi kuma sun yi kira ga kotun da ta sallame su ba tare da wani sharaddi ba.

An dai cabke wadannan sojoji ne tare da tsare su tun a watan Oktoban da ya gabata.