An samu karin matsaloli a aikin rejistar masu zabe a Nijeriya

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega,Shugaban Hukumar zabe ta Najeriya

Rahotanni daga Nijeriya na nuna cewa ana cigaba da samun matsalar a yunkurin rijistar masu zabe bayan da akai zargin cewa wasu matsa na sace na'urorin yin rijistar masu zaben.

Rahotanni sun ce a jihohin Lagos da Benue, da ma wasu jihohin Nijeriya an rawaito cewa matasa na sace akwatunan zabe.

Haka nan kuma ana ta cin karo da matsaloli wajen aikin sabunta rijistar masu zaben a Najeriyar.

Wata sabuwar matsala da aka lura da ita yanzu haka ita ce ta yiwa wasu mutanen rejista ba tare da an dauki hoton zanen yatsun su ba.

Haka kuma akwai rahotanni da ke nuna cewa wasu na yin rijistar fiye da sau daya, duk kuwa da cewa hukumomin zaben kasar na gargadin kaucewa hakan.

Hukumar zaben mai zaman kanta - INEC ta ce duk wanda ya yi rijistar ba tare da an dauki hoton zanen 'yan tsayunsa ba, to ya dauka tamkar bai yi ba ne.

Haka kuma wanda yayi rijistar sama da sau daya, to zai yi biyu babu.

Sannan kuma ta ce sace na'urori da dangwala yatsu ba za su yi tasiri ga masu rijista ba, ballantana ga bababn zabe kasa.