An haramtawa Terry jones zuwa Burtaniya

Image caption Wasu masu zanga zanga a yankin Punjab a Pakistan

An haramtawa malamin kiristan nan na Amurka Terry Jones da ya bayyana aniyar kona alkur'ani mai tsarki , shiga Burtaniya.

Gwamnatin Burtaniyar ta ce ba ta son ba da izinin shiga kasar ga wandanda zasu iya tada zaune tsaye.

Mr Jones ya yi kudirin ziyarar Burtaniya ne bisa gaiyatar wata kungiyar masu ra'ayin rikau, mai taken Ingila ta mu ce.

Terry Jones ya shaidawa BBC cewa babu hujjar hana shi shiga kasar, saboda ya na da 'yancin yin addinin da ya ke so tare da furta. ra'ayinsa.

A bara ne dai Mr jones ya sanar cewa zai kona alkur'ani mai tsarki abun da kuma ya janyo kakkausar suka da kuma zanga zanga a wasu kasashen duniya.