Sabuwar gwamnatin Tunisia ta yi zaman farko

Masu zanga-zanga
Image caption Masu zanga-zanga suna fatan rushewar jam'iyyar RCD ta Ben Ali

Sabuwar gwamnatin wucingadi tana taronta na farko na Majalisar Ministoci, mako guda bayan masu zanga-zanga sun hambarar da tsohon shugaban kasar, Zine El Abidine Ben Ali.

Da farko an jingine taron ne bayan bambance-bambancen da aka ba da rahoton samu a kan muhimman ma'aikatun da aka ba 'yan tsohuwar gwamnatin.

'Yan adawa dai sun ki shiga cikin sabuwar gwamnatin, suna son ganin lalle sai an kakkabe duk wani kusa na tsohuwar gwamnatin.

Gidan talabijin na Tunisiar ya ba da rahoton murabus din dukkan ministoci takwas na gwamnatin wucin gadi daga jam'iyyar ta RCD ta tsohon shugaba Ben Ali.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da samun tashin hankali, inda 'yan sanda a suka yi harbin gargadi don tarwatsa masu zanga-zanga a tsakiyar Tunis, babban birnin kasar.

Karin bayani