Rage ma'aikatun ba zai yi tasiri ga ci gaban Najeriya ba

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullunm a Najeriya na ganin cewa, magance cin hanci da rashawa, ita ce hanya mafi a'ala wajen samun ci gaban kasar, ba wai rage ma'aikatun gwamnati ba.

A jiya ne dai Majalisar mashawartan shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ta bukace shi da ya rage kudin da ake kashewa a tafiyar da gwamnati.

Shugaban majalisar, Theopilus Danjuma ya ce ya kamata gwamnatin ta soke wasu ma'aikatu tare da hade wadansu don amfani da kudin tafiyar da su wurin aiyukan ci gaban al'umma.

Manazarta dai na nuna damuwa game da girman gwamnatin Najeriya, inda su ka ce kasar na kashewa jami'an gwamnati fiye da abinda ta ke kashewa a samar da kayayyakin more rayuwa.

Jami'an diplomasiyya sun ce 'yan siyasar Najeriya na cikin wadanda suka fi yawan albashi a duniya.