'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga zanga a Algiers

Masu zanga zanga a kasar Algeria
Image caption Masu zanga zanga a babban birnin Algeria na Algiers wadanda ke neman karin 'yancin walwala

'Yan sanda a kasar Algeria sun tarwatsa wasu daruruwan masu zanga zanga a Algiers, babban birnin kasar, wadanda ke kiran da a ba su karin 'yancin walwala

An raunata masu zanga zangar da dama, an kuma ce an kama wasu daga cikinsu.

Jagoran jam'iyyar adawa ta RCD , wadda ta kira zanga zangar, ya ce cikin wadanda aka raunata har da jagoran jam'iyyar a majalisar dokoki.

An dai haramta yin zanga zangar, inda aka baza 'yan sanda masu dimbin yawa, da motoci masu sulke, na jiran ko-ta-kwana, haka nan kuma jiragen helikwafta sun rika shawagi a yankin.

Zanga zangar ta biyo bayan tarzomar da aka yi a birane da dama kan tsadar kayan abinci.