Rikicin siyasa a Bauchi

Rikicin siyasa a Bauchi

A jihar Bauchi da ke Najeriya majalisar dokokin jihar ta ce wa'adin shugabannin kananan hukumomin da ta dakatar a baya ya kare tun a watan Nuwamban.

Jiya ne dai majalisar dokokin ta yanke wannan shawara, inda ta ce, binciken da ta gudanar ya nuna mata cewa, shugabannin kananan hukumomin basu da wata hujja ta ci gaba da kasancewa a matsayinsu.

Sai dai majalisar dokokin ba ta fito karara ta ce shugabannin kananan hukumomin su sauka daga kan kujerunsu ba, saboda shari'ar da ake yi a game da batun.

Shugabannin kananan hukumomin sun ce wa'adinsu bai kare ba sakamakon dakatarwar da majalisar ta yi musu a baya, don haka ne ne suka tafi kotu domin ta yanke hukunci.