Shugabannin Kungiyar ECOWAS zasu gana a Bamako

Shugabanin kungiyar ECOWAS
Image caption Shugabannin kasashen Afrika ta yamma na kungiyar ECOWAS sun hallara a Bamako, babban birnin kasar Mali

Shugabannin kasashen Afrika ta yamma na kungiyar ECOWAS sun hallara a Bamako, babban birnin kasar Mali domin tattunawa kan rikicin siyasar kasa Ivory Coast.

Ana sa ran zasu yanke shawara kan ko zasu sauke wani aminin Laurent Gbagbo da ya ki sauka daga mulki, daga kan mukaminsa na gwamnan babban bankin Afrika ta yamma.

A cikin kwanaki masu zuwa ne ake sa ran takunkumin tarayyar turai zai fara aiki a kan gwamnan babban bankin, Phillipe-Henry-Tabley .

Abokin adawar Laurent Gbagbo, a shugabancin kasar, Alassane Ouattara, ya ce Mr Gbagbo ya debi miliyoyin daloli daga bankin, tun bayan zaben watan Nuwamban bara.