Tsohon shugaban Haiti na son a sasanta

Mr duvalier kenan lokacin da ake kaishi kotu
Image caption Mr Duvalier ya bukaci a sasanta tsakanin 'yan kasar

Tsohon shugaban Haiti Jean-Claude Duvalier, ya yi kira ga 'yan kasar su sasanta da juna.

Ya yi kiran ne a lokacin da yake hira da manema labarai ta farko tun bayan komowarsa kasar ranar Lahadi.

Mista Duvalier ya shafe shekaru ashirin da biyar yana gudun hijira.

Ya ce dawowarsa Haiti ta faru ne sakamakon mummunar girgizar kasar da ta yi fama da ita a bara, da kuma son ganin ya taimaka an sake gina kasar.

Sai dai kuma ya tabo irin yadda ya gudanar da mulkin kasar mai cike da kace-nace, matsayin da aka tunbekeshi daga kai a shekarar 1986, inda ya ce yana bakin cikin yadda wasu ke ganin gwamnatin da ya jagoranta ta yi masa illa.

Ana tuhumarsa ne da laifukan gallazawa bil adama, da kuma almundahana, tun bayan dawowarsa kasar.Kuma ya musanta zargin

Daya daga cikin lauyoyinsa ya ce, Mista Duvalier ba shi da niyyar sake barin kasar duk kuwa da tuhumar da ake yi masa, inda ya kara a cewa watakila ma ya sake fadawa cikin harkokin siyasa.

Mr Duvalier dai ya koma Haiti ne a yayin da kasar ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a zagaye na biyu bayan da wanda aka gudanar a baya ya cije.