Jam'iyyar PDP zata gudanar da zaben fidda gwani zagaye na biyu

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta ce za ta gudanar da zaben fidda gwani zagaye na biyu na gwamnoni a jahohin Kano da kuma Kogi.

Jamiyyar PDP tace zata yi hakanne sakamakon korafe korafen da ta samu a zaben fidda gwanin da aka yi a wadanan jahohin. Za'a gudanar da zaben a ranar ashirin da biyar ga watan janairu

Haka kuma jam'iyyar zata sake zaben fidda gwani zagaye na biyu da suka shafi wasu mazabun majalisar dattawa a jihohin Sokkoto, oyo da Bauchi da Taraba da Adamawa, Delta da kuma Kogi