Wani dattijo a kasar Saudiyya ya bankawa kansa wuta

Sarki Abdallah na Saudiyya
Image caption Wani mutum dan shekaru sittin ya bankawa kansa wuta a lardin Jizan na kasar Saudi Arabiya

Jami'ai a kasar Saudiyya sun ce wani mutum dan sama da shekaru sittin ya mutu bayan da ya banka wa kansa wuta a lardim Jizan, na kudancin kasar.

Jami'ai Sun ce suna gudanar da bincike kan dalilan da suka sa shi yin hakan.

Lamarin ya auku ne bayan jerin wasu abubuwan makamantansa, inda mutane ke banka wa kansu wuta a kasashen Larabawa, a matsayin koyi da abinda wani mai sayar da kayan lambu ya yi a Tunisia, wanda ya kashe kansa, lamarin da ya rura wutar yi wa gwamnatin tarzoma.

Rahotanni a kafafen yada labaran Saudiya sun ce mutumin na Jizan ya cinna ma kansa wuta ne ta hanyar amfani da man fetur, kuma ya cika a asibiti daga bisani.