Fira Ministan Tunisia zai yi ban-kwana da harkokin siyasa

Mohammed Ghannouchi
Image caption Ghannouchi zai yi ban-kwana da siyasa

Fira Ministan Tunisia Mohammed Ghannouchi, ya ce zai fice daga harkokin siyasa idan kasar ta koma kan turbar Dimokaradiyya.

A lokacin da ya ke jawabi a hirar da aka watsa ta gidan tabalijin din kasar ranar Juma'a, Mista Ghannouci ya yi alkawarin gudanar da abin da ya kira zaben farko da za a yi a kasar, wanda zai fi karbuwa ga kowa da kowa.

Ya ce bayan gudanar da zaben ne, shi kuma zai yi ban-kwana da harkokin siyasar kasar.

Mista Ghannouchi ya kuma yi alkawarin cewa a lokacin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da zaben, za a kawar da duk wata doka da ta sabawa mulkin dimokaradiyya.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata dai, masu zanga-zanga a Tunisia na cigaba da kiran a kawar da duk wadanda suka taka rawa a gwamnatin da ta gabata