Ana cigaba da zanga zanga a Tunisia

kasar Tunisia
Image caption Dubban jama'a a kasar Tunisia ciki har da 'yan sanda na zanga zanga

Dubban jama'a ciki har da wasu jami'an 'yan sanda sun bi tituna suna zanga zanga a Tunis, babban birnin Tunisia, inda cikin bukatun da suke nema har da murabus din gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Wani wakilin BC a Tunis ya ce abin mamaki ne yadda 'yan sanda suka shiga zanga zangar, ganin cewa mako guda da ya wuce su ne ke kare gwamnatin da aka hambaras ta Zinel el-Abidine Ben Ali.

Ministocin gwamnatin rikon kwaryar na wani taron gaggawa, bayan da Firaminista Muhammad Gannouchi ya bayyana a jiya cewa zai yi ritaya daga harkokin siyasa, bayan mika mulki ga zababbiyar gwamnati.