Harin Isra'ila kan jiragen agaji bai keta doka ba

Ehud Barak, ministan tsaron Isra'ila
Image caption Ehud Barak, ministan tsaron Isra'ila

Wani bincike kan harin da sojan Isra'ila suka kaiwa wani ayarin jiragen ruwa da ke dauke da kayan agaji zuwa Gaza, ya ce matakin bai sabawa dokokin kasa da kasa ba.

Hukumar da ta gudanar da binciken mai suna Turkel Commission, ta ce sojojin Isra'ila sun bude wuta ne domin kare kai.

Kasashen duniya sun yi suka sosai a kan harin da aka kai a shekarar da ta wuce, wanda yayi sanadiyyar mutuwar masu fafutuka 'yan kasar Turkiyya.

Ita ma Turkiyya ta gudanar da nata binciken, wanda ta mikawa majalisar dinkin duniya, inda ta zargi Isra'ila da yin sanadiyyar rasuwar mutane tara.