'Ba za a sauya ranar gudanar da zabe a Nijar ba'

Janar Saliou Djibo
Image caption Janar Djibo ya ce ba za sauya ranar gudanar da zabe a kasa rba

A Nijar, shugaban mulkin sojan kasar, Janar Saliou Djibo ya ce ba za a kara wa'adi kan ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokoki ba, wanda za a yi ranar 31 ga watan Janairu.

Shugaban ya yanke hukuncin ne jiya lokacin wani taron gaggawa da ya kira tare da 'yan siyasa domin yin nazari akan wata wasika da wasu 'yan takarar shugaban kasa suka aike masa.

Wasikar dai ta bukaci a dage zabukan na ranar 31 ga watan Janairu ne zuwa wani lokaci, ta yadda za a warware matsalolin da suka shafi yin zaben kafin a gudanar da shi.

Sai dai 'yan siyasa sun nuna rashin jin dadinsu kan wannan matakin da shugaban ya dauka, inda suka ce ya kamata shugaban ya yi la'akari da matsalolin da zaben ke fuskanta.