Da alamun kudancin Sudan zai balle

Salva Kiir, shugaban kudancin Sudan
Image caption Salva Kiir, shugaban kudancin Sudan

Kusan kashi 90 cikin 100 na mutanen da suka kada kuri'ar raba gardama a kudancin Sudan, sun bukaci yankin ya sami 'yancin kai, yayin da aka kirga kusan dukan kuri'un da aka kada.

Hukumar shirya kuri'ar raba gardamar ta Sudan ce ta sanar da wannan sakamako na wucin gadi, bayan ta kirga dukkanin kuri'u a arewacin kasar da kuma kasashen ketare, sannan da kusan kashi 99 na kuri'un da aka kada a kudancin kasar.

Ana sa ran fitar da cikkaken sakamakon zaben a farkon watan Fabrairu.

Idan wannan sakamako na wucin gadi ya tabbata, yankin kudancin Sudan na hanyar zama kasa ta 54 a nahiyar Afrika, nan gaba a cikin wannan shekarar.