Wikileaks a kan marigayi 'Yar adua

Marigayi Umaru Musa 'Yar adua
Image caption Marigayi Umaru Musa 'Yar adua

Shafin Wikileaks mai kwarmata bayanan sirri ya fitar da wasu bayyanai dangane da rashin lafiyar tsohon shugaban Najeriya, marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar adua, da kuma sauran abubuwan da suka biyo baya.

Shafin na Wikileaks ya ce, marigayi 'Yardua yayi fama da ciwon koda kafin rasuwarsa, abinda ya kai ga yi masa dashen koda tun lokacin da yana gwamnan jahar sa ta Katsina.

A cewar Wikileaks din, marigayin ya je Saudiyya a shekara ta 2002 domin a yi masa dashen kodar.

Bayyanan na Wikileaks sun kuma nuna cewa, launin fatar jikin marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yar adua ya sauya ne, saboda magungunan da ya rika sha don kodar da aka dasa masa ta sami karbuwa ga jikin sa.

A watau Mayun bara ne ya rasu, kuma Dr Goodluck Jonathan ya maye gurbinsa na shugaban Najeriya.