Ba'a fara rajistar masu zabe ba a wasu jihohin Najeriya

A Najeriya a daidai lokacin da aka shiga rana ta goma da fara aikin rijistar masu zabe, har yanzu Hukumar Zaben kasar ba ta fara aikin rijistar a wasu yankunan kasar ba.

Hukumar Zaben a jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriyar, ta tabbatarwa da BBC cewa, karancin kayan aikin da ta fuskanta ya sa sai a yammacin yau ne take saran tura kayan aikin zuwa wasu sassan jihar da dama.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jama'a ke ci gaba da nuna fargaba a sassa daban-daban na kasar game da yadda aikin ke gudana.

Da yake magana da BBC ta wayar tarho, Kwamishinan zabe na jihar Nasarawa Alhaji Ahmad Makama, ya ce saba alkawari da daya daga cikin kamfanonin da Hukumar ta baiwa kwangilar sayo na'u'rorin yin rijistar ya yi, shi ne abin da ya haifarwa da hukumar matsala.

Ya ce amma suna saran fara aikin a irin wadannan yankuna daga Gobe Talata.

Mai magana da yawun hukumar, Mr. Nick Dazen ya ce hukumar za ta tattauna domin duba irin matsaloli daga nasarorin da aka samu da nufin duba yiwuwar kara wa'adin rajistan ko akasin haka.

Tun farko dai jama'a sun nuna damuwa ganin yadda aka shafe kwanaki goma da fara aikin amma har yanzu ba su ido biyu da ma'aikatan

Wannan matsala dai ba a Nasarawa kawai ta tsaya ba, kamar yadda Abubakar Sani wani mazaunin karamar hukumar Marika a jihar Niger, ya shaidawa BBC.

BBC ta kuma samu korafe-korafe makamantan wadannan a jihohin Kaduna da Taraba da kuma birnin tarayya Abuja.

A yanzu dai yan kasar da dama dai sun zubawa Hukumar ido don ganin matakan da za ta dauka domin shawo kan matsalolin.