An kashe mutane 5 a jahar Plateau

Jami'an tsaro a Jos
Image caption Jami'an tsaro a Jos

A Najeriya, rahotanni daga jihar Plateau sun ce, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari a wasu kauyuka dake karamar hukumar Jos ta Kudu.

An ce sun kashe mutane 5 daga cikin mazauna kauyukan, kana suka jikkata da dama.

Jiya da dare ne aka kai wannan hari, wanda daya ne daga cikin jerin tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa da jihar ta Filato ta dade tana fama da su.

Hukumomin tsaro a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin.

Suka ce sun himmatu domin gano wadanda suka kai harin, ko da shike dai ana zarginsu da yin sakaci.