An fallasa sirri kan dangantakar Palasdinawa da Is'raila

Masu zanga-zangar nuna kiyayya ga Is'raila
Image caption An fallasa takardu kan dangatakar Palasdinu da Is'raila

Wasu takardun sirri da aka fallasa akan tattaunawar samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya sun nuna cewa, bangaren Palasdinawa ya taba amincewa a bayan fage da mamayar da Isra'ila ta yiwa kusan dukkan yankunan gabashin birnin Kudus.

Gidan talabijin din Aljazeera da kuma jaridar Guardian da ke London ne dai suka wallafa takardun.

Takardun sun nuna cewa, gwamnatin Palasdinawa ta baiwa Isra'ila wannan gagarumar dama ne a shekara ta 2008.

Takardun sun nuna yadda Isra'ila ta sanar da wasu shugabannin gwamnatin Palasdinu aniyarta ta kaddamar da yakin a yankin Gaza a shekara ta 2008 da kuma shekara ta 2009.

Bayanai da na nuna cewa, nan da kwanakin dake tafe za'a fitar da karin wasu takardun sirrin da dama da suka shafi irin yadda gwamnatin Paladinawa take musayar bayanan sirri na tsaro tsakaninta da gwamnatin Isra'ila.

'Martani kan fitar da takardun sirrin'

Babban mai shiga tsakani a bangaren Palasdinawa, Saeb Erekat ya bayyana shakku akan sahihancin takardun sirrin da aka kwarmata.

Mista Erekat ya fadawa gidan talabijin na Al Jazeera cewa, babu wani abin boyewa a yadda gwamnatin Palasdinu ke tafiyar da sha'aninta, kuma yace takardun da aka fallasa na cike da batutuwan da ba na gaskiya ba.

Sai dai Balarabiya 'yar majalisar dokokin Isra'ila, Haneen Zoabi ta ce, wadannan bayanai da aka kwarmata ka iya shafar halascin gwamnatin Palasdinawa.