Babu ruwanmu da zabukan da PDP za ta kara gudanarwa- INEC

A Najeriya, shirin da jam`iyyar PDP mai mulkin kasar ke yi don fara gudanar da zabukan fid-da-gwani don cike gurbi a wasu jihohin kasar gobe Talata ka iya fuskantar cikas, saboda hukumar zaben kasar ta ce ba za ta sa-ido a kan zabukan ba.

Hukumar zaben dai ta ce zabukan sun saba da ka`ida, kasancewar lokacin da ta kebe don gudanar da zabukan fid-da-gwanin ya wuce.

Sai dai jam`iyyar PDPn ta ce za ta gudanar da zabukan ne da nufin yin adalci ga wasu da suka gabatar da korafe-korafen bayan zabukan fid-da-gwanin da ta gudanar a baya.

Hukumar zaben Najeriyar dai ta bayyana cewa ita ma da wai-wai ta ji labarin cewa jam`iyyar PDPn za ta fara gudanar da zabukan fid-da-gwani don cike gurbi wasu `yan takararta na mukamin gwamna a jihohin Kano da Kogi, da kuma senata a sassan wasu jihohi takwas na kasar.

Alkalami ya riga ya bushe

Kuma a cewar hukumar wadannan zabukan cike-gurbi da PDP ke shirin yi ba da ita ba, duk kuwa da cewar hakin sa-ido a kan zabukan ya rataya ga wuyanta.

Mr Nick Dazang Mataimakin daraktan yada labarai na hukumar,ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe dangane da batun zaben fid-da-gwani; "Mu dai zaben bai shafe mu ba, kuma ba za zamu je mu sa'ido ba, saboda zaben ya keta doka".

Wakilin BBC ya yi kokarin jin martanin jam`iyyar Pdpn dangane da wannan matsayi na hukumar zabe ta hanyar tuntubar shugaban jam`iyyar na kasa, Dr Bello halliru da kakakinta, farfesa Rufa`i Ahmed Alkali ta wayar salula, amma babu wanda ya amsa daga cikinsu.

Tun da farko dai jam`iyyar, cikin wata sanarwar da kakakin ya sanya mata hannu ta bayyana cewa ta yanke shawarar gudanar da zabukan fid-da-gwanin ne sakamakon korafe- korafen da ta samu daga `ya`yanta bayan zabukan fid-da-gwanin da ta yi a baya.

Matakin da ta ce zai taimaka wajen tabbatar da adalci da hada-kan jam`iyyar wuri guda. Sai dai wannan hanzarin za a iya cewa bai samu shiga a wurin hukumar zaben ba.

Jam`iyyar PDPn dai ta sha caccaka da suka daga wasu `ya`yanta tun lokacin da ta bayyana aniyarta ta sokewa da kuma gudanar da zabukan fid-da-gwani don cike guraban.

Ga misali, jiya a jihar Kano har zanga-zanga wasu suka yi bisa zargin cewa an soke zaben dantakar mukamin gwamna ne ba sididi ba sadada, a jihar sai don a huce haushin kayen da shugaban kasar ya sha a babban taron jam`iyyar na kasa, ganin cewa bai kwashe nika da waka ba a hannun wakilan jihar Kano.

Kazalika wasu na zargin cewa jam`iyyar ta soke wasu zabukan fid-da-gwani na takarar senata a wasu jihohin ne ganin wasu da ake wa kallon `yan mowa a majalisar dattawan kasar ba su samu tikitin sake tsayawa takara a karkashin tutar jam`iyyar ba a zabe mai zuwa. Zargen-zargen da jam`iyyar a matakai daban-daban ta musanta.