A hukunta masu hannu a rikicin Plateau

Rikicin Jos
Image caption Rikicin Jos

Hukumar kare hakkin bil-adama ta Majalisar dinkin duniya ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta tabbatar da ta zakulo mutanen da ke da hannu a rikice-rikicen da ake fama da su a jihar Plateau a 'yan watannin nan, tare da hukunta su.

Hukumar kare hakkin bil-adamar ta Majalisar ta yi wannan kira ne, bayan da kungiyar nan ta kare hakkin bil-adama a Najeriya da ake kira SERAP, ta gabatar da kuka a gaban Majalisar, a kan rikice-rikicen na Plateau.

A 'yan shekarun nan daruruwan mutane ne suka hallaka, kuma dimbin dukiya ta salwanta, a tashe tashen hankula a jahar Plateau, wadanda ake dangantawa da addini da kabilanci da kuma siyasa.