Zanga-zanga na kamari a Tunisia

Masu zanga-zanga a Tunisia

A Tunusia daruruwan masu zanga-zanga sun yi dafifi a ofishin Fira Ministan kasar da ke birnin Tunis, duk da dokar hana fitar dare da aka sanya.

Mutanen dai na neman gwamnatin rikon kwaryar kasar da ke cike da masu nasaba da tsohon shugaban kasar, Zainul Abidin Ben Ali ta yi murabus.

Masu zanga-zangar sun ce, za su ci gaba da kasancewa akan titunan kasar, sai duk wadanda su yi aiki da rusasshiyar gwamnatin kasar da suka hada Fira Minista, Muhammed Al Ghannouchi sun yi murabus daga gwamnati.

Masu zanga-zangar ne dai suka yi sanadiyar tserewar Zainul Abidin daga kasar.