Rikicin siyasar Lebanon

Masu zanga zanga a Lebanon

Majalisar dokokin Lebanon na cigaba da zaben sabon Fira Minista, duk da fusatar da 'yan Sunni da ke goyon bayan mai rikon mukamin, Sa'ad Hariri su ka yi.

Su dai 'yan Sunnin sun kira wata zanga-zanga a yau Talata, yayin da kungiyar Hizbullah ta 'yan Shi'a ke dab da tabbatar da ganin wani hamshakin mai kudi da ya yi karatu a Amurka, Najib Mikati ya zama sabon Firaminista

Dama dai magoya bayan Sa'ad Hariri na nuna rashin amincewarsu da yiwuwar kafa gwamnatin da 'yan Hizbullah suka yi kaka-gida a cikinta.

An gudanar da zanga-zanga a yankunan daban-daban na arewacin Lebanon, inda 'yan Sunni suka fi yawa.