Majalisar wakilan Najeriya ta dawo daga hutu

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majalisar wakilan Najeriya za ta koma daga hutu

A Najeriya, a yau ne ake sa ran majalisar wakilan kasar za ta koma zama bayan hutun da 'yan majalisar suka yi na karshen shekarar 2010.

Majalisar na komawa bakin aiki ne yayin da ake korafe-korafe akan aikin rijistar masu zabe da ke gudana yanzu haka a duk fadin kasar.

Hounourable Labaran Yunusa Danbatta dan majalisar wakilan Najeriyar ne, ya shaidawa BBC cewa majalisar za ta maida hankali ne kan batutuwa daban-daban, wadanda zasu ciyar da kasar gaba.

Ya ce babban abin da za su kammala muhawara akai shi ne kasafin kudin shekarar 2011, wanda shugaban kasa ya mikawa majalisar kafin ta fara hutu.

Honourable Danbatta ya ce majalisar za ta yi muhawara kan korafe-korafen da mutane ke yi kan yadda aikin rijistar masu zabe ke tafiya, da zummar ganin hukumar zabe ta kara lokacin gudanar da aikin.