Majalisar Wakilan Nijeria ta yi gyara a dokar zabe

Majalisar dokokin Nijeriya
Image caption Majalisar dokokin Nijeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta yi gyara a dokar zaben kasar domin baiwa hukumar zabe damar kara wa'adin yiwa 'yan kasar rajistar samun katin zabe.

Sai dai a nata bangaren, majalisar dattijan kasar ta ce ba za ta yi garajen yin gyara a dokar ba, har sai ta ji ta bakin shugabannin hukumar zaben tukunna.

A don haka majalisar dattijan ta gayyaci shugaban hukumar zaben Attahiru Jega ya bayyana a gabanta gobe domin yi ma ta bayani.

Wata majiya a hukumar zaben ta ce hukumar tana ci gaba da tattara bayanai a kan yadda aikin yake tafiya a sassa daban-daban na kasar domin yanke shawarar ko za ta bukaci kara wa'adin aikin ko kuma a'a.